Najeriya - Kaduna

Gwajin likitoci ya nuna gwamnan Kaduna ya kamu da cutar coronavirus

Gwamnan jihar Kaduna Malam Nasir El-Rufai.
Gwamnan jihar Kaduna Malam Nasir El-Rufai. AFP / Pius Utomi EKPEI

Gwamnan jihar Kaduna dake arewacin Najeriya Malam Nasir El Rufa’I, ya bayyana kamuwa da cutar coronavirus da ta zama ruwan dare game duniya bayan kutsawa cikin kasashe 183.

Talla

Gwamnan da bakinsa ya bayyana haka a wani sakon bidiyon da ya aike ta shafinsa na dandalin sada zumunta Facebook.

Cikin bidiyon, El- Rufa’I da yace gwajin likitoci ne ya bada tabbacin kamuwar tasa, inda yace a yanzu haka ya killace kansa domin baiwa na kusa da shi kariya.

Gwamnan ya kuma bukaci al’ummar jihar Kaduna da su ci gaba da bin dokar hana fita ta tsawon sa’o’i 24 da ya kafa, domin dakile yaduwar annobar tsakanin jama’a.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.