Gwamnatin Jihar Kaduna ta kama wasu limamai
Gwamnatin Jihar Kaduna dake Najeriya ta kama wasu limamai guda biyu da suka bijirewa dokar hana fita wajen jagorancin Sallar Juma’ar da aka gudanar jiya.
Wallafawa ranar:
Sanarwar gwamnatin Jihar tace an kama Malam Aminu Umar Usman da Malam Umar Shangel dake Unguwar Malali da kuma Unguwar Kanawa ne saboda sabawa dokar hana bude wuraren ibada da gwamnatin jihar ta sanar domin yaki da cutar coronavirus ko kuma COVID-19.
Gwamnatin tace za’a gurfanar da su a gaban kotu domin yi musu shari’a kamar yadda doka ta tanada.
Yayin da gwamnatin ke yabawa jama’ar jihar da suka mutunta dokokin da ta sanar, tace duk wanda ya karya dokar zai gamu da fushin hukuma ba tare da nuna banbanci ba.
Gwamnatin tace har yanzu dokar hana fita na tsawon sa’oi 24 na nan daram, kuma jami’an tsaro zasu cigaba da tababtar da ita.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu