Najeriya

Gwamnatin Legas ta janye dokar hana fitar dare

Gwamnan jihar Legas Babajide Sanwo-Olu ya sanar da janye dokar hana fitar daren da yayi shelar za ta soma aiki daga ranar lahadi 29 ga watan maris domin dakile annobar coronavirus.

Wani sashin birnin Legas dake kudancin Najeriya.
Wani sashin birnin Legas dake kudancin Najeriya. Reuters / Akintunde Akinleye
Talla

Yayin sanarwar gwamnan yace za a yi amfani da damar ce wajen tsaftace wuraren taruwar jama’a da sinadarai, sai dai daga bisani yace bayan sauraron shawarar kwararru ne ya yanke shawarar janye dokar, la’akari da cewa sinadaran da za a yi amfani da su ba masu guba bane.

Tuni dai cibiyar bincike da dakile yaduwar cutuka ta Najeriya, ta ce yawan wadanda suka kamu da cutar coronavirus a kasar ya karu zuwa 89 daga 81, bayan samun karin mutane mutane 8 a yau asabar.

An dai gano karin mutanen ne a jihohin Legas inda mutane 7 suka kamu, yayinda kuma a karon farko aka samu wanda annobar ta shafa a Benue.

A birnin Legas da ya fi ko’ina a Najeriyar adadin wadanda annobar ta shafa a yanzu haka jimillar mutane 59 ne suka kamu da cutar, 3 a Ogun, 2 a Edo, Rivers guda 1, sai kuma Oyo guda 3 Osun 1, sai kuma mutane 14 da suka kamu a Abuja.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI