Coronavirus

Karin mutane 8 sun kamu da coronavirus a Najeriya

Daya daga cikin jami'an dake baiwa wani asibiti tsaro a birnin Lagos dake Najeriya, yayin tsaftace hannun masu ziyarar marasa lafiya.
Daya daga cikin jami'an dake baiwa wani asibiti tsaro a birnin Lagos dake Najeriya, yayin tsaftace hannun masu ziyarar marasa lafiya. Pius Utomi Ekpei/AFP — Getty Images

Cibiyar bincike da dakile yaduwar cutuka ta Najeriya, ta ce yawan wadanda suka kamu da cutar coronavirus a kasar ya karu zuwa 89 daga 81, bayan samun karin mutane 8 a ranar asabar.

Talla

An dai gano karin mutanen ne a jihohin Legas inda 7 suka kamu, yayinda kuma a karon farko aka samu wanda annobar ta shafa a Benue.

A baya bayan nan ne dai annobar ta bulla a yankin arewa maso gabashin Najeriya, bayan gano mutane 2 da suka kamu a jihar Enugu.

A birnin Legas da ya fi ko’ina a Najeriyar adadin wadanda annobar ta shafa, a yanzu haka jimillar mutane 59 ne suka kamu da cutar, 3 a Ogun, 2 a Edo, Rivers guda 1, sai kuma Oyo guda 3, Osun 1, sai kuma mutane 14 da suka kamu a Abuja.

Sauran jihohin da annobar ta shafa sun hada da Bauchi inda mutane 2 suka kamu, sai kuma jihar Ekiti mai mutum 1 da annobar ta shafa.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI