Najeriya

'Yan Sandan Katsina sun yi arrangama da matasa bayan kama limami

Wasu jami'an 'yan sandan Najeriya.
Wasu jami'an 'yan sandan Najeriya. AFP

Rahotanni daga Jihar Katsina dake Najeriya sun ce mutum guda ya ran sa, yayin da wasu suka samu raunuka lokacin da aka samu arangama tsakanin jami’an Yan Sanda da matasa a karamar hukumar Kusada.

Talla

Bayanai sun ce matasan sun fusata ne lokacin da Yan Sandan suka je gidan wani limami Malam Hassan domin kama shi dangane da bijirewa umurnin gwamnati wajen jagorantar Sallar Juma’a a jiya.

Wannan mataki ya sa suka yiwa ofishin Yan Sandan tsinke domin kubutar da shi abinda ya kaiga arangama tsakanin su da jami’an Yan sanda.

Kakakin Yan Sandan Jihar Gambo Isah ya tabbatar da aukuwar lamarin, inda yace matasan sun kona musu ofishi da motoci guda 7 da kuma Babura guda 10.

Isah yace an dada jami’an tsaro a garin kuma tuni aka kama matasa sama da 90 daga cikin wadanda suka shiga tarzomar, yayin da guda ya rasa ran sa.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI