Najeriya-Coronavirus

Dokar hana fita a Legas, Ogun da Abuja za ta fara aiki a daren yau

Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari.
Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari. Reuters

Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari, ya bada umarnin hana fita a jihohin Legas, Ogun da kuma Abuja, har tsawon makwanni 2 domin hana yaduwar annobar coronavirus da ke ci gaba da hallaka rayuka a sassan duniya.

Talla

Buhari ya bada umarnin ne a ranar lahadi, yayin jawabin da ya gabatar wa ‘yan kasar kan matakan da gwamnati ke dauka domin yakar annobar murar.

Shugaban Najeriyar ya ce dokar hana fitar a jihohin na Legas, Ogun da kuma Abuja za ta soma aiki daga karfe 11 na daren ranar litinin, 30 ga watan maris na shekarar 2020 da muke ciki.

Buhari, ya kara da bada umarnin dakatar da tafiye-tafiye tsakanin ilahirin jihohin kasar na tsawon makwannin 2 cikin har da jiragen saman fasinja.

Yanzu haka dai alkalumman cibiyar dakile yaduwar cutuka ta Najeriya sun bayyana karuwar adadin wadanda suka kamu da cutar coronavirus a kasar zuwa 111, bayan samun karin mutane 14 da annobar ta shafa.

Gwajin likitoci ya gano sabbin mutanen da suka kamun ne a Abuja, Kaduna, Osun da kuma Oyo.

Sanarwar cibiyar dakile yaduwar cutukan ta Najeriya, ta ce 2 daga cikin sabbin mutanen sun kamu ne a Abuja, 1 a Kaduna; gwamnan jihar Malam Nasir El Rufa’i, sai kuma a jihar Osun inda nan mutum 1 ya kamu, yayinda annobar murar ta shafi mutane 4 a jihar Oyo.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.