Coronavirus

Coronavirus ta sake kisa a Najeriya

Gwamnatin Najeriya ta sanar da mutun na biyu da cutar Coronavirus ta kashe a kasar a daidai lokacin da aka sallami mutane 5  da cutar ta kama a jihar Lagos bayan sun warke.

Jami'an da ke yaki da Coronavirus a Najeriya
Jami'an da ke yaki da Coronavirus a Najeriya Quartz
Talla

Ministan Lafiya, Osagie Ehanire ya sanar da mutuwar mutum na biyun a yayin zantawarsa da manema labarai a babban birnin Abuja.

Adadin wadanda suka warke daga wannan cuta ya kai 8 bayan an samu mutum biyar da suka warke a Lagos, inda aka ba su kulawa ta musamman a asibitin Yaba wanda gwamnatin jihar da kuma Hukumar Yaki da Cututtuka ta Kasa ke kula da shi.

Yayin da suke yabawa da irin matakan da aka dauka wajen kula da su, mutanen da suka warken sun bukaci hukumomin Najeriya da su bai wa jami’an kula da lafiyar da ke cibiyar, inshorar lafiya domin kare su ganin irin hadarin da ke tattare da ayyukansu.

Jihar Lagos ke sahun gaba wajen samun masu dauke da cutar COVID-19 inda ta samu mutane 68 da suka kamu da ita, sai kuma Abuja mai 21.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI