Coronavirus

Najeriya ta yi wa dubban mutane gwajin Coronavirus

Daya daga cikin cibiyoyin gwajin Coronavirus a jihar Lagos
Daya daga cikin cibiyoyin gwajin Coronavirus a jihar Lagos tv360nigeria

Hukumomin Najeriya sun sanar da yi wa mutane sama da 2,000 gwaji domin sanin halin da suke ciki dangane da cutar Coronavirus ko kuma COVID-19, kuma kasa da kashi 10 ne daga cikinsu aka gano suna dauke da cutar.

Talla

Darakta Janar na Hukumar Yaki da Cututtuka na kasar, Chikwe Ihekweazu ya  bayyana cewa, hukumar na farautar wasu mutane kusan 6,000 da suka yi mu’amala da wadanda suka kamu da cutar domin yi musu gwaji.

Ya zuwa yanzu dai mutane 111 aka bayyana suna dauke da cutar a Najeriya, kuma 68 daga cikin suna jihar Lagos, 21 a Abuja, sai Oyo mai mutane 7.

Sauran sun hada da jihar Ogun mai mutane 3, Osun da Enugu da Edo da Bauchi na da mutane biyu-biyu, sai Ekiti da Benue da Kaduna da Rivers masu mutum guda-guda.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.