Najeriya

Buhari ya wuce makadi da rawa a dokar Lagos- Soyinka

Fitaccen marubuchin Najeria Farfesa Wole Soyinka ya zargi shugaban kasa Muhammadu Buhari da wuce makadi da rawa wajen kafa dokar hana fita a jihohin Lagos da Abuja da Ogun don dakile yaduwar Coronavirus.

Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari
Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari RFI Hausa
Talla

A wata sanarwar da ya rabawa manema labarai da ya yi wa lakabi ‘tsakanin cutar COVID da sabawa kundin tsarin mulki’, Farfesa Soyinka ya ce, yana kyautata zaton Buhari ya wuce huruminsa wajen kafa dokar.

Soyinka ya ce, zai zama abin takaici idan jama’a suka bijire wa dokar da aka kafa saboda rashin bin ka’ida, duk da yake wannan lokaci ne na bukatar hadin kai domin cimma biyan bukata.

Marubuchin ya ce kafin daukar irin wannan matakin, yana da kyau masana harkar shari’a su yi bayani ko matakin da shugaban ya dauka ya dace ko kuma a’a.

Soyinka wanda shi ma ya killace kansa, ya ce Najeriya ba ta cikin yanayin yakin da za a sanya mata irin wannan doka, saboda haka ya zama wajibi a hada kai wajen hana shugabannin karya doka.

Marubucin ya bayyana cewar ana zargin shugaban da ya yi batar dabo ko kuma tserewa daga bakin aikinsa, da farkawa daga barci wajen bada umurni.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI