Najeriya

Coronavirus ta kara bazuwa a Najeriya

Cibiyar yaki da Coronavirus a jihar Lagos.
Cibiyar yaki da Coronavirus a jihar Lagos. REUTERS/Temilade Adelaja

Hukumomin Najeriya sun sanar cewa an sake samun karuwar masu dauke da cutar COVID-19 guda 4 a cikin kasar, abin da ya kawo adadin wadanda suka kamu da ita zuwa 135.

Talla

Hukumar Yaki da Cututtuka a Najeriya ta ce, sabbin mutane hudu da aka samu dauke da cutar sun fito ne daga jihohin Ogun da Osun.

Adadin mutanen da suka kamu da cutar a Najeriya ya tashi zuwa 135, yayin da mutane 2 suka mutu, kama 8 suka warke daga ita.

Wannan ya nuna cewar, yanzu haka babu wata jiha da ke yammacin Najeriya da ba a samu bullar cutar ba, yayin da jihar Lagos ke sahun gaba da mutane 81, sai kuma Abuja mai mutane 25.

Alkaluman da hukumomin Najeriya suka bayar sun nuna cewa,  mutane 8 ke dauke da cutar a Oyo, cikin su har da gwamnan jihar Seyi Makinde, sai kuma Osun mai mutane 5, Ogun nada mutane 4, sai Kaduna mai mutane 3 cikinsu har da gwamna Nasir El Rufai.

Jihohin Bauhi da Enugu da Edo na da mutane biyu-biyu har da gwamna Bala Muhammed, sai kuma Rivers da Benue da ke da mutun guda-guda.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.