Dokar hana fita ta fara aiki a Lagos da Abuja
Al’ummomin Lagos, Abuja da Ogun a Najeriya, sun share daren farko zaune a gidajensu, bayan da dokar hana fita tsawon makonni biyu ta fara aiki da misalin karfe 11 na daren da ya gabata don hana yada cutar Coronavirus.
Wallafawa ranar:
Adadin wadanda suka kamu da cutar a Najeriya ya tashi zuwa 131 bayan da aka samu karin mutane 20 da suka kamu da ita a ranar Litinin, yayin da adadin wadanda suka rasa rayukansu ya tashi zuwa biyu a fadin kasar.
Alkalumman Cibiyar Yaki da Cututtuka ta kasar sun nuna cewa, an samu karin mutanen ne a jihohin Lagos, Kaduna, Oyo da kuma Abuja
Kamar yadda alkalumman cibiyar suka nuna, a jihar Lagos kawai an samu mutane 13, sai 4 a Abuja, 2 a Kaduna yayin da aka samu mutum daya a jihar Oyo, yayin da wasu bayanai ke cewa wanda aka sama a Oyo ba wani ba ne face gwamnan jihar Seyi Makinde.
Kafin samun karin wadannan mutane 20 a jiya, dama akwai mutane 111 da ke dauke da kwayar cutar ta Covid-19 a jihohin Lagos, Abuja, Ogun, Kaduna, Oyo, Edo, Bauchi, Enugu, Osun, Ekiti, Rivers da kuma Benue.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu