Najeriya

Sakin El-Zakzaky shi ne zaman lafiyar Najeriya- 'Yan Shi'a

Jagoran mabiya  Shi'a a Najeriya El-Zakzaky
Jagoran mabiya Shi'a a Najeriya El-Zakzaky RFI HAUSA

Mabiya Kungiyar ‘Yan uwa Musulmi a Najeriya sun yi barazanar tayar da hankalin kasar muddin wani mummunan al'amari ya cika da shugabansu Sheikh Ibrahim El- Zakzaky.

Talla

Wannan ya biyo bayan matsalar da aka samu a gidan yarin Kaduna, inda ake tsare da El-Zakzaky.

Jagoran Shi’a  jihar Sokoto, Malam Sidi Maniru ya shaida wa RFI hausa cewa, sakin jagoran shi ne zaman lafiyar Najeriya kamar dai yadda jama’rsu da dama suka sha fadi a ceawrsa.

Kuna iya latsa alamar sautin da ke kasa domin sauraren muryar shugaban Shi’a a Sokoto, Malam Sidi Maniru.

Sakin El-Zakzaky shi ne zaman lafiyar Najeriya- 'Yan Shi'a

Malam Sidi ya bayyana cutar coronavirus a matsayin babbar barazana ga Sheikh El-Zakzaky da ke tsare a hannun hukumomin Najeriya, yana mai cewa, wasu kasashen duniya sun sallami fursunoninsu don hana yaduwar coronavirus.

Wannan na zuwa ne bayan rahotanni sun ce, an samu hatsaniya a wani kurkukun jihar Kaduna, inda fursunoni suka yi yunkurin fasa gidan yarin don tserewa da nufin kauce wa kamuwa da cutar coronavirus.

Sheikh El-Zakzaky da matasa Zeenat na tsare a wannan gidan yarin da ke Independent Way a Kaduna.

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.