Najeriya

Amurkawan da ke guje wa coronavirus sun makale a Najeriya

Filin jirgin sama na kasa da kasa na Murtala Mohammed dake birnin Lagos.
Filin jirgin sama na kasa da kasa na Murtala Mohammed dake birnin Lagos. REUTERS/Akintunde Akinleye/File Photo

Daruruwan Amurka da suka shirya ficewa daga Najeriya daga a ranar Juma’a sun makale a filin jiragen sama na Murtala Mohd da ke birnin Lagos, inda suka yi ta dakon isowar jirgin da zai fara kwashe su zuwa gida.

Talla

Rahotanni sun ce, daga bisani Amurkawan sun fusata da rashin isowar jirgin, abin da ya tilasta musu komawa gidaje da ote-otel din da suke zaman haya a Najeriya.

An dai bayyana cewa, jirgin saman Omni Air ne aka shirya cewa, zai iso  daga Dulles don kwashe Amurkawan, amma ya gaza isa Najeriya a ranar Juma'a saboda wasu dalilai da suka hada da yadda wasu kasashen suka ki amince masa ratsawa ta cikinsu.

Duk da cewa, Amurka ce kasar da ta fi fama da masu dauke da cutar coronavirus a duniya, amma ta zamo kasa ta baya-bayan da take shirin kwashe al'ummarta daga Najeriya.

Cutar ta kashe fiye da mutane dubu 6 a Amurka, yayi da mutane biyu kacal suka mutu a Najeriya a sanadiyar annobar.

A bangare guda, ‘yan asalin Birtaniya dubu 4 da ke zaune a Najeriya su ma sun shigar da bukatarsu ta ficewa daga kasar domin komawa gida.

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI