Coronavirus ta kashe wata 'yar Kano a Amurka
Wallafawa ranar:
Karamin Jakadan Najeriya a birnin New York na Amurka, Benaoygha Okoyen ya tabbatar da mutuwar ‘yan Najeriya uku da suka hada da wata Bakanuwa bayan kamuwa da cutar coronavirus .
Mista Okoyen ya ce, Hajiya Laila Abubakar Ali mai shekaru 60 ‘yar asalin jihar Kano, ta rasu ne a ranar 25 ga watan Maris a daidai lokacin da take jinya a asibitin Lincoln da ke Bronx a New York sakamakon kamuwa da coronavirus.
Kazalika akwai wani likita dan asalin jihar Abia wanda shi ma cutar ta kashe bayan ya kamu da ita a bakin aikinsa na kula da marasa lafiya a na birnin New York da ke zama cibiyar coronavirus a Amurka.
Sai kuma Bassey Offiong mai shekaru 25, dan asalin jihar Calabar kuma dalibi da ke ajin karshe a sashen koyar da fasahar harhada sinadarai na Jami’ar Western Michigan da shi ma ya yi ban-kwana da duniya a sanadiyar annobar.
Gwamnatin Najeriya ta mika ta’aziyarta ga iyalan mamatan.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu