Najeriya

Buhari ya bada umarnin sakin fursunonin Najeriya

Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari.
Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari. oodweynemedia

Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya bada umarnin sakin fursunoni dubu 2 da 600 a sassan kasar, a wani mataki na rage cinkoson gidajen gyaran hali a daidai lokacin da ake fargabar yaduwar cutar coronavirus.

Talla

Ministan Cikin Gida, Ra’uf Aregbesola ya sanar da wannan shirin a yayin taron manema labarai na duniya da ya gudana a wannan Alhamis a birnin Abuja.

Ministan ya ce, daga cikin fursunonin da za su ci gajiyar shirin, har da mutane 885 da aka garkame su bayan sun gaza biyan tarar da aka yanke musu ta jumullar Naira miliyan 21.4, kudin da gwamnatin kasar ta ce, za ta biya a madadinsu.

Ministan Shari'ar Najeriya, Abubakar Malami ya ce, Majalisar Dinkin Duniya ta shawarci kasashen duniya mambobinta da su rage cinkoson gidajen yarinsu saboda aiwatar da tsarin bada tazara tsakanin al'umma don kauce wa kamuwa da coronavirus.

Ministan ya bayyana afuwar da shugaba Buhari ya yi wa fursunonin a matsayin wani al'amari mai cike da tarihi.

Sai dai ministan ya koka kan cewa, kashi 70 na fursunonin Najeriya na dakon a yanke musu hukunci, abin da ya sa suke ci gaba da zama ba tare da sanin makomarsu ba.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI