Najeriya

Gwamnan Bauchi ya warke daga coronavirus

Gwamnan jihar Bauchi Bala Mohammed cikin annashuwa
Gwamnan jihar Bauchi Bala Mohammed cikin annashuwa ThisDay

Gwamnan Jihar Bauchi Sanata, Bala Mohammd ya warke daga cutar coronavirus bayan gwajin da aka sake yi masa a ranar Alhamis ya nuna cewa, cutar ta rabu da shi.

Talla

Wannan na zuwa ne bayan kwanaki 16 da aka tabbatar cewa, ya kamu da cutar murar mashakon kamar yadda sakamako ya nuna a gwajin da Hukumar Yaki da Cutuka ta Najeriya, NCDC ta yi masa.

A shafinsa na Twitter, gwamnan ya mika godiya ga Allah da daukacin mutanen da suka tsaya masa a lokacin da ya kasance a killace don jinyar wannan cuta.

Ya zuwa daren jiya Alhamis, an tabbatar cewa, cutar ta COVID-19 ta harbi jumullar mutane 288 a Najeriya, sannan an sallami 51 daga cibiyar kula da masu dauke da cutar, inda kuma mutun bakwai suka mutu.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.