Najeriya

Ana fargabar wani mutun ya rarraba wa mutane corona a Kaduna

Gwamnan jihar Kaduna Malam Nasir El-Rufai ya sanar da kamuwa da coronavirus makwanni da suka wuce
Gwamnan jihar Kaduna Malam Nasir El-Rufai ya sanar da kamuwa da coronavirus makwanni da suka wuce REUTERS/Afolabi Sotunde

Gwamnatin Jihar Kaduna da ke Najeriya ta bayyana fargabar cewa, wani mutun da ya kamu da cutar coronavirus a garin Mando, ya yada ta tsakanin al’umma, lura da cewa, bai jima da dawowa daga jihar Lagos ba a cikin motar haya.

Talla

Kwamishiniyar Lafiyar Jihar, Dr. Amina Mohammed Baloni ta bayyana mutum a matsayin mai aikin gadi kuma tuni aka killace shi a cibiyar yaki da cutuka masu yaduwa ta jihar.

An  gane cewa, yana dauke da cutar ce bayan rashin lafiyarsa ya tsananta, yayin da Kwamishiniyar Lafiyar ke cewa, abu ne mai matukar wahala da sarkakiya, a iya bin diddigin mutanen da ya yi hulda da su musamman fasinjojin da suka shiga mota tare da shi tun daga jihar Lagos.

Kazalika mara lafiyar ya yi jerin zirga-zirga a cikin jihar kaduna cikin motocin haya  daban daban bayan dawowarsa daga Lagos.

A yunkurinta na dakile yaduwar cutar, gwamnatin Kaduna ta bukaci al’umma da su rika bada tazarar a huldarsu da jama’a, sannan ta bukaci direbobin motocin haya da su rika daukar mutun biyu a kan kowacce kujera da ke cikin mota.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.