Najeriya

Mun gano kwaryar tsafi cike da jini a Zamfara- 'Yan sanda

An gano kwarya cike da jini, sannan kuma ga sunayen fitattun 'yan siyasar jihar Zamfara a wani gidan tsafi da ke jihar.
An gano kwarya cike da jini, sannan kuma ga sunayen fitattun 'yan siyasar jihar Zamfara a wani gidan tsafi da ke jihar. buzzgh

Rundunar ‘yan sandan jihar Zamfara da ke Najeriya ta tabbatar da gano wata kwarya cike da jinin bil’adama daga wani mutun dan kungiyar asiri a garin Gusau.

Talla

Jami’in Hulda da Jama’a na Rundunar ‘Yan Sandan, Mohammed Shehu ya sanar da haka a yayin zantawa da manema labarai a yau Asabar.

A makon  jiya ne, rundunar ‘yan sandan ta kai samame gidan mutumin da ke wata unguwar masu hannu da shuni, bayan an kwarmata musu irin barnar da ake tafka wa a wannan gida.

A yayin wannan samame, jami’an ‘yan sandan sun gano kayayyakin tsafe-tsafe da suka hada da kwarya cike da jini da kuma wata takarda dauke da sunayen wasu fitattun ‘yan siyasa a jihar.

Yanzu haka ana ci gaba da gudanar da bincike kan al’amarin a cewar rundunar ‘yan sandan Zamfara.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.