Kano-Najeriya

Gwamnatin Kano za ta takaita cinkoso a Masallatai

Abdullahi Umar Ganduje, gwamnan jihar Kano a Najeriya.
Abdullahi Umar Ganduje, gwamnan jihar Kano a Najeriya. africatodaynewsonline

Gwamnatin Kano ta bayyana shirinta na takaita cinkoson jama'a a daukacin Masallatan Juma'a da ke fadin jihar, a wani mataki na dakile yaduwar annobar coronavirus wadda aka tabbatar da bullarta a karshen mako a jihar.

Talla

Gwamna Abdullahi Umar Ganduje ya tabbatar da wakilinmu Abubakar Isa Dandago da shirinsu na takaita taruwar jama'a a Masallatan.

Kuna iya latsa alamar sautin da ke kasa domin sauraren cikakken rahoton Dandago game da halin da Kanawa suka shiga bayan samun bullar coronavirus a karon farko a jihar.

Gwamnatin Kano za ta takaita cinkoso a Masallatai

Daga cikin matakan da gwamnatin ta ce, za ta dauka har da rufe wasu  kasuwanni a jihar.

Tun bayan da aka gano mutumin da ya kamu da cutar a jihar, jama’a ke bayyana fargabarsu kan yaduwar cutar musamman yadda bayanai ke cewar mara lafiyar mai shekaru 75 kuma tsohon jami'in gwamnati, ya yi mu'amala da mutane da dama kafin killace shi.

Tuni gwamnatin Kano ta ce, ta kara karfafa matakan tsaronta a kan iyakokin jihar.

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.