Najeriya

'Yan Najeriya na dakon makomar dokar hana fita ba

Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya bukaci 'yan kasar da su ci gaba da zama a gida don kauce wa kamuwa da coronavirus
Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya bukaci 'yan kasar da su ci gaba da zama a gida don kauce wa kamuwa da coronavirus REUTERS/Siphiwe Sibeko

'Yan Najeriya na dakon makomarsu dangane da tsawaita ko kuma kawo karshen dokar hana fita da gwamnatin tarayya ta kafa a jihohin Lagos da Ogun da kuma babban birnin Abuja. Da misalin karfe bakwai na yammacin yau ne shugaba Muhammadu Buhari zai gabatar da jawabi game da wannan batu.  

Talla

Ana ganin watakila shugaba Buhari ya tsawaita dokar, lura da yadda ake ci gaba da samun masu dauke da coronavirus a sassan kasar.

Tuni mazauna Abuja da Lagos da Ogun suka koka kan matakin killace su a gida, suna masu cewa, sun shiga wani mummunan hali saboda rashin isasshen abinci da sauran kayyakin masarufi.

Kuna iya latsa alamar sautin da ke kasa domin sauraren cikakken rahoton da wakilinmu Kabir Yusuf ya aiko mana daga Abuja, inda za ku ji korafin da 'yan Najeriya ke yi kan wannan doka.

Makomar dokar hana fita a Lagos

Kodayake gwamnatin Najeriyar ta ce, ta bullo da shirin tallafa wa masu karamin karfi a wannan lokaci da ake fuskantar koma-bayan tattalin arziki.

Sai dai da dama daga cikin wadanda ke sa ran samun wannan tallafi sun ce, babu abin da ya iso gare su.

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.