Najeriya

Coronavirus ta harbi 'yan Najeriya 86 a kwana guda

Jihar Lagos na sahun gaba wajen dauke da masu cutar coronavirus a Najeriya.
Jihar Lagos na sahun gaba wajen dauke da masu cutar coronavirus a Najeriya. Punch

Cibiyar Hana Yaduwar Cutuka a Najeriya, ta sanar da samun karin mutane 86 da suka harbu da cutar coronavirus a kasar, wanda shi ne karo na farko da aka samu irin wannan adadi a rana guda.

Talla

Cibiyar ta NCDC ta ce an samu karin mutane 70 a Lagos, 7 a Abuja, a jihohin Katsina da Akwa Ibom an samun karin mutane uku-uku, yayin da karon farko aka samu bullar cutar a jihohin Jigawa da Borno.

Har ila yau cibiyar ta NCDC, ta ce kashi 40% na wadanda cutar ta kashe sun mutu ne a cikin makon jiya.

A jumulce, mutane 627 ne suka harbu da cutar COVID-19 a Najeriya, amma 170 sun warke.

An gano karuwar masu dauke da cutar ce a daidai lokacin da jama'a a sassan Najeriya ke zaman gida na dole, matakin da mahukunta suka dauka da zummar hana yaduwar cutar a bainal jama'a.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.