Ilimi Hasken Rayuwa

Matashin da ya kera na'urar numfashi a Bauchi

Sauti 10:38
Engr. Faisal Sani Bala
Engr. Faisal Sani Bala RFI Hausa

Shirin Ilimi Hasken Rayuwa na wannan makon tare da Bashir Ibrahim Idris ya tattauna ne da wani matashin injiniya kuma malami a Jami'ar Abubakar Tafawa Balewa da ke jihar Bauchi a Najeriya, Engr. Faisal Sani Bala, wanda ya kera na'urar Ventilator da ke taimaka wa mara lafiya shakar numfashi a daidai lokacin da kasashen Afrika ke fama da karancin na'urar duk da cewa, a irin wannan lokacin na annobar coronavirus aka fi bukatar na'urar.