Najeriya

Legas: Za a yiwa gawarwaki jana'izar bai daya nan da mako 2

Wani dakin ajiye gawarwaki da aka fi sani da mortuary a turance. (An yi amfani da wannan hoto domin misali kawai)
Wani dakin ajiye gawarwaki da aka fi sani da mortuary a turance. (An yi amfani da wannan hoto domin misali kawai) AFP

Sakamakon hana zirga zirga da kuma tarukan jama’a, wuraren ajiye gawarwaki a asibitocin dake Legas dake Najeriya sun cika, hakan tasa gwamnatin Jihar shirin gudanar da jana’izar gama gari domin samun karin fili.

Talla

Gwamnan Legas Babajide Sanwo-Olu, ya bukaci wadanda suke da ‘yan uwa a dakin ajiye gawarwakin da su shirya jana’izarsu, domin babu dokar da ta hana yin jana’izar.

Gwamnan yace muddin mutane suka gaza zuwa su dauki gawarwakin ‘yan uwansu, gwamnati za ta yi musu jana’izar bai daya nan da makwanni biyu masu zuwa.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.