Bakonmu a Yau

Gwamnonin arewacin Najeriya sun soma daukar matakan hana Almajirci

Sauti 03:35
Sakamakon wani bincike da aka gudanar a shekarar 2017, ya nuna cewar akwai kananan yara da suka hada da Almajirai da kuma mabarata miliyan 3 a jihar Kano kadai.
Sakamakon wani bincike da aka gudanar a shekarar 2017, ya nuna cewar akwai kananan yara da suka hada da Almajirai da kuma mabarata miliyan 3 a jihar Kano kadai. AFP/AMINU ABUBAKAR

Gwamnonin Arewacin Najeriya sun dauki matakin kawo karshen almajiranci da kuma mayar da almajirai jihohi ko kuma kasashen da suka fito.Wannan na zuwa ne a daidai lokacin da kasar ke fuskantar kalubalen annobar COVID-19.Tuni wasu jihohin suka fara kwashe almajiran suna mayar da su jihohi da kuma kasashen da suka fito.Dangane da wannan mataki, Bashir Ibrahim Idris ya tattauna da Dr Aliyu Tilde, kwamishinan ilimi na Jihar Bauchi, wanda yayi karin bayani kan matakan da suke bi wajen aiwatar da shirin.