Najeriya

Majalisa ta baiwa Buhari damar karbo bashin naira biliyan 850

Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari a zauren majalisar dokokin kasar.
Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari a zauren majalisar dokokin kasar. Femi Adeshina/ Facebook

Majalisar dattijan Najeriya ta amince da bukatar shugaban kasar Muhd Buhari na karbo bashin naira biliyan 850.

Talla

Cikin wasikar da ya aikewa ‘yan majalisar, shugaba Buhari yace gwamnati za ta karbi bashin ne a cikin gida, wanda za a yi mafani da shi wajen aiwatar da ayyukan dake kunshi cikin kasafin shekarar bana.

Rahotanni sun ce yayin zama kan bukatar karbo bashin ‘yan majalisar dattijan sun cimma matsayar jingine aiwatar da wasu matakai da aka sabi bi, domin gaggauta aminewa da bukatar, la’akari da yanayin da kasa ke ciki.

Ranar talata 8 ga watan oktoban shekarar 2019, shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya gabatar da kudurin kasafin shekarar 2020 na Naira Tiriliyan 10.33 ga zaman hadin guiwa da ya kunshi mambobin majalisar tarayyar kasar.

Sai dai a shekarar ta bana, gwamnatin Najeriya ta zaftare kasasfin kudinta da akalla naira biliyan 2, bayan yaduwar cutar coronavirus a sassan duniya da kuma tasirin annobar da ya durkusar da tattalin arzikin kasashe, ciki harda Najeriya da ta dogara kan man fetur wajen samun kudaden shiga.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.