Bakonmu a Yau

'Yan Najeriya na caccakar gwamnati kan salonta na yakar coronavirus

Sauti 03:31
Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari.
Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari. Twitter/Asorock

‘Yan Najeriya na cigaba da korafi dangane da yadda hukumomin kasar ke tunkarar shawo kan annobar coronavirus dake cigaba da yaduwa da kuma lakume rayukan jama’a.Daga cikin matsalolin da ake korafi akai akwai rashin gwajin jama’a domin sanin matsayinsu dangane da cutar, musamman a Jihar Kano, inda a kwanakin baya bayan nan aka shaida mutuwar mutane da dama cikin kankanin lokaci, koda yake hukumomi sun ce mace-macen basu da alaka da annobar coronavirus.Caccakar hukumomin na Najeriya na zuwa ne, a dai dai lokacin da shugaban kasar Muhammadu Buhari ya bada umurnin killace jama’ar Jihar kano da kuma tura mata kayan aiki da ma’aikatan da take bukata domin shawo kan matsalar.Kan wannan mataki ne kuma Bashir Ibrahim Idris ya tattauna da Hon Sani Zoro, tsohon dan Majalisar Tarayya a Najeriya.