Najeriya-Coronavirus

An killace Alaramma da dalibansa a Bauchi

Wasu kananan yara yayin karatun allo (An yi amfani da wannan hoto kan wannan labari domin misali kawai)
Wasu kananan yara yayin karatun allo (An yi amfani da wannan hoto kan wannan labari domin misali kawai) Reuters

Yayinda a Najeriya gwamnonin jihohin arewa ke musayar daruruwan almajiran dake komawa jihohinsu na asali, a wani mataki na takaita yaduwar annobar Coronavirus a makarantun tsangaya, da kuma aiwatar da matakan hana barace-barace a yankin arewacin kasar, hukumomin lafiya a jihar Bauchi, sun tabbatar da killace wani Alaramma da wasu almajiransa dake nuna alamun kamuwa da cutar ta coronavirus, bayan da aka maida su gida.Daga Bauchin, wakilinmu Shehu Saulawa ya aiko mana da karin bayani a rahotonsa.

Talla

An killace Alaramma da dalibansa a Bauchi

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.