Coronavirus-Kano

Ganduje ya roki gwamnatin Najeriya da ta sassauta dokar hana fita a Kano

Gwamnan jihar Kano Abdullahi Umar Ganduje tare da jagororin tawagar kwararrun da gwamnatin tarayyar Najeriya ta aika da ita Kano domin yakar annobar coronavirus.
Gwamnan jihar Kano Abdullahi Umar Ganduje tare da jagororin tawagar kwararrun da gwamnatin tarayyar Najeriya ta aika da ita Kano domin yakar annobar coronavirus. RFIHAUSA/Abubakar Dangambo

Gwamnan Kano Abdullahi Umar Ganduje, ya roki gwamnatin tarayyar Najeriya da ta sassauta dokar hana fita ta tsawon makwanni 2 da ta kafa a jihar, domin dakile yaduwar annobar coronavirus.

Talla

A ranar litinin 27 ga watan Afrilu, shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya bada umarnin kulle jihar ta Kano ba shiga ba fita, zalika babu zirga-zirga tsawon makwanni 2, daga bisani kuma shugaban ya aike da tawagar kwararrun likitoci don gaggauta kawo karshe cutar.

Buhari ya killace Kano ne kwanaki kalilan bayanda gwamna Ganduje ya koka kan cewar gwamnatin tarayyar Najeriya ta yi watsi da Kano ta fuskar taimaka mata wajen yakar annobar ta coronavirus.

Sai dai yayin kaddamar da soma aikin tawagar kwararrun likitocin ta musamman a ranar alhamis, gwamna Ganduje ya nemi da a sassauta dokar kullen, domin saukakawa al’ummar jihar halin matsin da suka shiga sakamakon tsayar hada-hadar kasuwanci, ayyuka, da sauran harkokin yau da kullum.

Yanzu haka dai Kano ta zama jiha ta 2 bayan Legas da yawan masu dauke da cutar coronavirus a Najeriya, bayanda a ranar alhamis hukumar yaki da cutuka ta Najeriya NCDC ta sanar da samun karin mutane 80 da suka kamu da cutar a jihar, adadin da a jimlace ya kai 219, 5 daga cikinsu kuma sun mutu.

Yanzu haka dai jimillar mutane dubu 1 da 932, daga cikinsu 58 sun mutu, yayinda 319 suka warke.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.