Najeriya-Kano

Daya daga cikin sabbin Sarakunan Kano ya rasu

Mai martaba Sarkin Rano, marigayi Alhaji Tafida Ila Autan Bawo.
Mai martaba Sarkin Rano, marigayi Alhaji Tafida Ila Autan Bawo. Solacebase

Allah ya yiwa Sarkin Rano dake jihar Kano a Najeriya, Alhaji Tafida Abubakar Ila Auta Bawo ya rasuwa a yau asabar.

Talla

Sarkin ya rasu yana da shekaru 74, bayan gajeruwar jinya a wani asibiti dake jihar Kano.

Makusantan Sarkin sunce kafin mutwarsa an kwantar da shi a asibiti a ranar Juma’ar da ta gabata.

A daren yau ake sa ran yi masa jana’iza a gidansa dake masarautarsa ta garin Rano.

Alhaji Tafida Abubakar Ila Auta, daya ne daga cikin sabbin Sarakuna masu daraja ta daya, da gwamnatin Kano karkashin Dakta Abdullahi Umar Ganduje ta karawa matsayi, bayan kirkirar sabbin masarautu hudu masu daraja ta farko a jihar.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.