Najeriya-Coronavirus

Har yanzu babu maganin da muka amince da shi kan coronavirus - NAFDAC

Wata mata yayin kokarin tantance bayanan ingancin wani magani, ta hanyar amfani da wayar hannu.
Wata mata yayin kokarin tantance bayanan ingancin wani magani, ta hanyar amfani da wayar hannu. REUTERS/handout/Sproxil

Hukumar kula da ingancin abinci da magunguna a Najeriya ta NAFDAC, tace ya zuwa yanzu bata amince da wani magani da za’ayi amfani da shi wajen kula da masu dauke da cutar coronavirus ko COVID-19 ba.

Talla

Shugabar Hukumar Mojisola Adeyeye, tace bata baiwa wani kamfani ko wata hukuma izinin amfani da wani magani ko rigakafi ba a Najeriya.

Adeyeye tace yayinda ake cigaba da gudanar da bincike a matakin duniya, Najeriya tare da Hukumar Lafiya ta Duniya WHO sun tashi tsaye wajen ganin an gano magani ko rigakafin kamuwa da cutar, inda ta bukaci jama’a da su yi taka-tsan-tsan wajen amfani da maganin da ba’a tantance ba.

Shugabar hukumar tace NAFDAC kadai ke da alhakin amincewa da duk wani magani ko rigakafi a Najeriya.

Sanarwar hukumar na zuwa ne bayan da takwararta ta Amurka, ta amince da maganin Remdesivir a matsayin maganin cutar, yayinda shi kuma Gwamnan Bauchi dake Najeriya Bala Muhammed ya bada umurnin amfani da Chloroquine a Jiharsa domin kula da masu dauke da cutar coronavirus.

Gwamnan yace maganin na Chloroquine akayi ta amfani da shi wajen kula da shi lokacin da ya kamu da cutar.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.