Coronavirus-Kano

Kano: Karin mutane 92 sun kamu da coronavirus a kwana 1

Gwamnan Jihar Kano Dakta Abdullahi Umar Ganduje yayin duba wani rahoto kan cutar coronavirus.
Gwamnan Jihar Kano Dakta Abdullahi Umar Ganduje yayin duba wani rahoto kan cutar coronavirus. RFI Hausa/Abubakar Isa Dandago

Hukumar yaki da yaduwar cutuka ta Najeriya NCDC tace a ranar Juma’ar da ta gabata kadai, an samu karin mutane 92 da suka kamu da cutar coronavirus a Kano, adadi mafi yawa da jihar ta gani tun bayan samun rahoton bullar cutar cikinta a watan Afrilu.

Talla

Yanzu haka dai yawan masu dauke da cutar coronavirus a Kano ya kai 311, adadi mafi yawa a tsakanin jihohin Najeriya bayan a Legas, mai jimillar mutane dubu 1 da 6 da suka kamu.

Sabbin alkalumman na nuni da cewa sannu a hankali Kano na rufe tazara ko gibin da Legas ta bata wajen yawan masu dauke da cutar ta COVID-19.

A makon da ya gabata ne dai jihar Kanon ta fuskanci koma baya a yakin da take da annobar, bayanda tsirarun cibiyoyin gwajin cutar suka fuskanci karancin kayan aiki, sai kuma wasu daga cikin jami’an lafiyar dake tawagar yaki da annobar ta coronavirus da suka kamu da cutar, abinda ya janyo rufe cibiyoyin gwajin zuwa wani lokaci.

Ba a jima da rufe wuraren gwajin ba ne kuma al’ummar Kano suka shaida mutuwar mutane da dama da suka hada da fitattu dama wadanda ba a san su ba, abnda ya jefa tsoron cikin zukatan jama’a, gami da fargabar ko mace macen na da alaka da annobar murar ta coronavirus.

A ranar litinin shugaban Najeriya Muhd Buhari ya bada umarnin killace jihar ta Kano tsawon makwanni 2, tare da tura tawagar kwararrun likitoci domin kawo karshen annobar, matakin da ya farfado da ayyukan cibiyoyin gwajin cutar, gami da kafa wasu sabbi a jihar.

Dangane da batun karuwar bazatar da adadin masu dauke da cutar ta coronavirus da ake gani a Kanon kuwa, wasu kwararru na lakanta hakan da farfado da cibiyoyin gwajin cutar, da kuma bijirewar da wasu mutane ke yiwa gargadin likitoci kan kiyaye abinda zai taimakawa annobar wajen yaduwa.

Yayin zantawa da sashin Hausa na RFI, Dr. Salihu Ibrahim Kwaifa, kwararran likita a birnin Abuja, ya ce, lallai al'amari akwai tayar da hankali, sai dai shi ma yace hakan baya rasa nada da rashin kiyaye matakan kariyar da ya kamata a dauka, da kuma farfadowar aikin yiwa jama’a gwajin cutar.

Dr Salihu Ibrahim Kwaifa kan karuwar masu cutar coronavirus a Najeriya

 

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.