Najeriya-Coronavirus

Sassauta dokar hana fita kuskure ne - Kungiyar likitoci

Wasu matasa yayin wasan kwallon kafar kan titi a birnin Legas dake kudancin Najeriya, yayin aikin dokar hana fita.
Wasu matasa yayin wasan kwallon kafar kan titi a birnin Legas dake kudancin Najeriya, yayin aikin dokar hana fita. REUTERS/Temilade Adelaja

Kungiyar likitocin Najeriya ta bayyana matakin gwamnatin kasar, na sassauta dokar hana fitar da aka kafa a jihohin Legas, Ogun da kuma birnin Abuja saboda annobar coronavirus a matsayin kuskure, matakin da tace sam bata goyi bayansa ba.

Talla

A ranar litinin 27 ga watan Afrilu, yayin jawabi ga ‘yan Najeriya, shugaban kasar Muhammadu Buhari ya sanar sassauta dokar hana fitar a jihohin uku, matakin da yace zai soma aiki daga ranar 4 ga watan Mayu.

Sai dai cikin sanarwar da kungiyar likitocin Najeriya ta fitar a baya bayan nan, dauke da sa hannun shugabanta dakta Franci Faduyile, tace yayi wuri gwamnati ta sassauta dokar hana zirga-zirgar, la’akari da cewar har yanzu akwai sauran rina a kaba, dangane da karancin mutanen da ake yiwa gwajin kamuwa da cutar coronavirus a rana ko mako guda, sai kuma karuwar adadin masu dauke da cutar da a kullum ake gani, adadin da a yanzu ya zarta dubu 2.

Kungiyar likitocin ta kare matsayinta na adawa da sassauta dokar hana fitar da karin hujjar cewa, kwanaki 7 kawai ya dauki annobar ta coronavirus ta kama karin mutane dubu 1 har da doriya, bayan kama rukunin mutane dubu na farko a Najeriya, dan haka akwai bukatar sake nazartar matakan da gwamnati ke dauka.

Sai dai matsayin kungiyar likitocin ya sha banban da na wasu jagororin Najeriya, da kuma wasu masu ruwa da tsaki kan sha’anin tattalin arziki, domin kuwa a makon da ya gabata gwamnonin Najeriya suka nemi shugaba Buhari da ya sassauta dokar hana fitar a Legas, Abuja da kuma Ogun, don ceto mutane daga halin kuncin da suka shiga.

Cikin wasikar da suka aikewa shugaban Najeriya Muhammadu Buhari, gwamnonin sun nemi da a tilastawa mutane rufe baki da hancinsu kafin fita, da kuma kiyaye hada cinkoson jama’a.

A ranar alhamis kuma 30 ga watan Afrilu, gwamnan Kano Abdullahi Umar Ganduje ya roki gwamnatin tarayyar Najeriya da ta sassauta dokar hana fita ta tsawon makwanni 2 da ta kafa a jihar, domin dakile yaduwar annobar coronavirus.

Ganduje yace sassauta dokar kullen, zai saukakawa al’ummar jihar halin matsin da suka shiga sakamakon tsayar hada-hadar kasuwanci, ayyuka, da sauran harkokin yau da kullum.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.