Najeriya

Allah ya yiwa Sarkin Kauran Namoda rasuwa

Marigayi Sarkin Kauran Namoda Alhaji Ahmad Muhammad Asha.
Marigayi Sarkin Kauran Namoda Alhaji Ahmad Muhammad Asha. Tribune Online

Mai marataba Sarkin Kauran Namoda dake jihar Zamfara, Alhaji Ahmad Muhammad Asha “Sarkin Kiyawan Kauran Namoda”, ya rasu da safiyar yau lahadi, bayan doguwar jinya.

Talla

Sarkin ya rasu yana da shekaru 71, bayan shafe lokaci mai tsawo yana fama da cutar sukari da kuma hawan jini.

Kani ga Sarkin marigayi, Dan jekan Kauran Namoda Alhaji AbdulKarim Ahmad Asha, yace likitoci sun shafe akalla kwanaki 4 suna kula da yayan nasa a fada inda ya samu murmurewa, amma daga bisani aka gaggauta maida shi asibiti, bayanda jikinsa ya sake rikicewa, inda yayi kwanaki 3 kafin Allah ya karbi rayuwarsa.

Kafin nada shi Sarkin Kauran Namoda a shekarar 2004, marigayi Alhaji Ahmad Muhammad Asha ya rike mukaman Daraktan Kudi da kuma Ma’aji, a kananan hukumomi da dama a jihar Zamfara, ciki harda Kauran Namoda da kuma Gusau.

Sarkin ya rasu ya bar mata uku da kuma ‘ya’ya 11.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.