Najeriya

Annobar coronavirus ta kashe dan majalisar Nasarawa

Dan majalisar dokokin jihar Nasarawa Adamu Suleiman, mai wakiltar karamar hukumar Nasarawa ta tsakiya.
Dan majalisar dokokin jihar Nasarawa Adamu Suleiman, mai wakiltar karamar hukumar Nasarawa ta tsakiya. Vanguard Nigeria

Annobar coronavirus ta kashe dan majalisa a Nasarawa Adamu Suleiman, wanda ke wakiltar karamar hukumar Nasarawa ta tsakiya a zauren majalisar dokokin jihar.

Talla

Dan majalisar shi ne mutum na farko da cutar ta halaka a jihar ta Nasarawa, tun bayan da ta bada rahoton bullar annobar a cikinta a farkon makon jiya.

Yayin tabbatarwa da manema labarai rahoton mutuwar dan majalisar dokokin a garin Lafia, gwamnan jihar Nasarawa Abdullahi Sule, yace Adamu Suleiman ya mutu ne tun kafin gwajin likitoci ya tabbatar da cewa ya kamu da cutar coronavirus.

Gwamna Abdullahi Sule yace a yanzu haka an killace daukacin iyalan dan majalisar da ya mutu, da sauran wadanda ke zaune a gidansa, zalika za a killace dukkanin wadanda suka yi masa jana’iza la’akari da cewar lokacin da suka yi hakan, ba’a tabbatar da cewa annobar coronavirus bace ta kashe shi, dan haka masu jana’izar basu kiyaye dokokin likitoci wajen mu’amala da gawarsa ba.

Gwamnan na Nasarawa ya kuma ce za a rufe zauren majalisar dokokin jihar, har sai an kammala tsaftace shi da sinadaren kashe kwayoyin cutar coronavirus ko kuma COVID-19.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.