Najeriya-Coronavirus

Jumillar mutane 85 coronavirus ta halaka a Najeriya

Wasu jami'an kiwon lafiya yayin daukar gawar shugaban ma'aikatan fadar shugaban Najeriya Malam Abba Kyari. 18/4/2020.
Wasu jami'an kiwon lafiya yayin daukar gawar shugaban ma'aikatan fadar shugaban Najeriya Malam Abba Kyari. 18/4/2020. Nigeria Presidency/Handout via REUTERS

Karin mutane 17 sun rasa rayukansu a Najeriya dalilin cutar coronavirus, abinda ya sanya jumillar adadin wadanda annobar ta halaka kaiwa 85 daga 68 a tsakanin ranar Juma’a zuwa asabar.

Talla

Cikin sanarwar da fitar a ranar asabar 1 ga watan Mayu, hukumar yaki da yaduwar cutuka ta Najeriya NCDC tace an samu karin mutane 220 da suka kamu da cutar a jihohin kasar 22.

A wannan karon jihar Legas ke jagorantar takwarorinta a yawan wadanda da suka kamu da cutar ta coronavirus, da adadin mutane 62, sai Abuja da mutane 52 da suka kamu, 31 a Kaduna, a Sokoto kuma mutane 13.

Jihar Kebbi na da mutane 10 da annobar ta harba, sai Yobe mai mutane 9, Borno mutane 6, Edo da Bauchi na da mutane 5-5, Gombe, Enugu, da Oyo mutane 4-4, sai kuma Zamfara mai mutane 3.

Sauran jihohin da suka bada rahoton karin mutanen da suka kamu da cutar coronavirus a Najeriya sun hada da, Nasarawa, Osun, Ebonyi, Kwara, Kano da kuma Filato dukkaninsu mutane bibbiyu.

Sabbin alkalumman ya sanya jumillar yawan wadanda suka kamu da coronavirus a Najeriya kaiwa dubu 2 da 388, daga cikinsu kuma 385 sun warke, yayinda 85 suka mutu.

Har yanzu dai Legas ke kan gaba a yawan jumillar wadanda suka kamu da cutar ta coronavirus a Najeriya da adadin mutane dubu 1 da 68, sai kano mai mutane 313, Abuja 266, Ogun 56, Osun 36, Katsina mutane 40, Edo, mutane 52, Akwa Ibom 16, Kaduna 66, Ekiti 11 sai Ondo mai muatne 13 da suka kamu.

Sauran jihohin sun hada da Rivers mai mutane 14, Delta 17, Jigawa guda 7, Bauchi 53, Gombe 96, Enugu 8, Abia 2, Niger 3, Zamfara 12, Taraba 8, Anambra da Benue na da mutum guda-duda, Adamawa mutane 4 suka kamu da coronavirus, sai Filato mai mutane 3, Yobe 13, Nasarawa mutane 9, Ebonyi 5, Bayelsa 5, Kebbi 12 sai kuma jihar Imo mai mutane 2.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.