Najeriya-Coronavirus

Dangote ya ginawa Kano katafariyar cibiyar gwajin coronavirus

Sabuwar cibiyar gwajin cutar Corona da za a iya yiwa Mutum 400 gwaji a rana guda da Alhaji Aliko Dangote ya gina a Kano.
Sabuwar cibiyar gwajin cutar Corona da za a iya yiwa Mutum 400 gwaji a rana guda da Alhaji Aliko Dangote ya gina a Kano. RFI Hausa/Abubakar Isa Dandago

Gidauniyar hamshakin attajirin nahiyar Afrika Alhaji Aliko Dangote, 'Dangote Foundation' ta baiwa gwamnatin jihar Kano tallafin wajen gwajin cutar coronavirus, wadda za a iya yiwa mutane 400 gwaji a rana guda.

Talla

Bayaga wajen gwajin na tafi da gidanka da aka samar a asibitin Muhammadu Buhari dake unguwar Giginyu, gidauniyar ta baiwa gwamnatin Kanon taimakon motocin daukar marasa lafiya 10, tare da kayan kariya daga cutar da likitoci zasuyi amfani dasu

A baya ma dai gidauniyar ta samar da wajen killace daruruwan masu dauke da cutar a filin wasa na sani Abacha

Alkalumman masu dauke da cutar coronavirus a jihar Kano dai ya kai 313, abinda ke kara jefa fargabar karin wadanda ke kamuwa, a daidai lokacin da mace mace ke yawaita a jihar, wadanda ake dangantawa da annobar ta coronavirus.

Zuwaira Yusufu babbar jami’a ce a gidauniyar ta Dangote Foundation, ta shaidawa wakilinmu Abubakar Isa Dandago cewar karuwar adadin wadanda ke kamuwa da cutar a jihar ta Kano na daga cikin dalilan da suka sanya Alhaji Aliko Dangote bada umarnin bada tallafin.

Zuwaira Yusufu kan gina katafariyar cibiyar gwajin coronavirus a Kano.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.