Najeriya-Coronavirus

Adadin mutanen da coronavirus ta kama a Najeriya ya zarce 2,500

Wasu matasa a kasuwar Wuse dake Abuja, babban birnin tarayyar Najeriya. 27/3/2020.
Wasu matasa a kasuwar Wuse dake Abuja, babban birnin tarayyar Najeriya. 27/3/2020. REUTERS/Afolabi Sotunde

Hukumomin Najeriya sun ce adadin mutanen da annobar coronavirus ta kama a kasar sun zarce 2,500, sakamakon samun karin mutane 170 a jiya, yayin da 87 suka mutu.

Talla

Alkaluman da hukumar yaki da cututtukar Najeriya suka bayar sun nuna cewar, a jiya lahadi mutane 170 suka kamu da cutar, kuma daga cikin su 39 sun fito ne daga Lagos sai 29 daga Kano, 24 daga Ogun, 18 daga bauchi, 15 daga Kaduna da kuma 12 daga Abuja da Sokoto.

Sauran sun hada da 8 a Katsina, 7 a Barno, 3 a Nasarawa, 2 a Adamawa da guda a Oyo, abinda ya kawo adadin wadanda suka kamu da cutar a Najeriya zuwa 2,558, kuma 87 daga cikin su sun mutu, yayin da 400 sun warke.

Wadannan alkaluma sun kuma nuna cewar Jihar Lagos ke sahun gaba da mutane 1,107, sai Kano mai mutane342, sai Abuja mai 278, Gombe 96, Barno 82, Kaduna 81, Ogun na da 80, Bauchi 71, Sokoto 66, Edo 52 sannan Katsina na da 46.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.