Bakonmu a Yau

COVID-19: Gwamnatin Borno ta kaddamar da shirin tallafawa marasa karfi

Sauti 02:59
Kwamitin bada agajin gaggawa a jihar Barno
Kwamitin bada agajin gaggawa a jihar Barno RFI Hausa

A wani mataki na ragewa al’umma radadin zaman gida don hana yaduwar annobar Korona, gwamnatin jihar Barno dake Najriya, ta fara rarraba kayayyakin abinci a Maiduguri da kewaye.Kwamitin da gwamnan jihar Farfesa Baba Gana Umaru Zulum ya daurawa alhakin gudanar da wannan aikin rabo, karkashin jagorancin kwamishin ayyukan noma Injiniya, Bukar Talba, ta fara aikin a wasu anguwannin birnin Maiduguri da suka hada da Gwange da Bolori.Dangane da haka ne Ahmed Abba ya zanta da kwamishina, kuma shugaban kwamitin rabon, Injiniya Bukar Talba, ga kuma yadda zantawarsu ta gudana.