Najeriya

COVID-19: Gwamnatin Nasarawa ta rufe majalisar dokokin jihar

Harabar zauren majalisar dokokin jihar Nasarawa.
Harabar zauren majalisar dokokin jihar Nasarawa. Vanguard Nigeria

Gwamnatin Nasarawa dake Najeriya ta bada umurnin rufe Majalisar Dokokin Jihar bayan mutuwar daya daga cikin Yan Majalisun ta Hon Adamu Suleiman Ibrahim sakamakon kamuwa da cutar coronavirus.

Talla

Yayin tabbatarwa da manema labarai rahoton mutuwar dan majalisar dokokin a garin Lafia, gwamnan jihar Nasarawa Abdullahi Sule, yace Adamu Suleiman ya mutu ne tun kafin gwajin likitoci ya tabbatar da cewa ya kamu da cutar coronavirus.

Gwamnan yace rufe Majalisar wani matakin kariya ne ga abokan aikin sa da kuma ma’aikatan dake aiki a Majalisar, yayin da shugaban Majalisar tare da abokan aikin su suka killace kan su saboda mu’amala da marigayin.

Gwamnan yace zasu cigaba da neman wadanda suka yi mu’amala da marigayin domin yi musu gwaji dan kare lafiyar su, yayin da ya bukaci jama’ar jihar da suka dawo daga wuraren da ake da cutar da su je a gwada su.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.