Dr Sani Gwarzo kan alakar mace-macen Kano da coronavirus

Sauti 03:38
Daya daga cikin makabartun dake karamar hukumar Fagge a jihar Kano.
Daya daga cikin makabartun dake karamar hukumar Fagge a jihar Kano. Daily Trust / Richard P. Ngbokai

Tawagar kwararrun da Gwamnatin Najeriya ta tura Jihar Kano domin kai mata dauki dangane da annobar coronavirus na can suna cigaba da ayyukan su.Yayin zantawa da wakilinmu Abubakar Isa Dandago a baya bayan nan Dr Sani Gwarzo, daya daga cikin tawagar kwararrun likitocin yace duk da cewa har yanzu suna kan bincike, sun soma samun kwararan hujjojin dake alakanta mace-macen da aka gani a jihar ta Kano da annobar coronavirus.