Najeriya-Coronavirus

Jami'an tsaro sun killace fadar Sarkin Daura saboda coronavirus

Harabar fadar Mai Martaba Sarkin Daura Alhaji Faruk Umar Faruk.
Harabar fadar Mai Martaba Sarkin Daura Alhaji Faruk Umar Faruk. Daily Trust

Gwamnatin Jihar Katsina dake Najeriya ta bada umurnin killace fadar Sarkin Daura saboda abinda ta kira yaduwar cutar coronavirus wadda ke cigaba da lakume rayuka.

Talla

Sakataren Gwamnatin Katsina Dr Mustapha Inuwa ya sanar da daukar matakin, saboda rahotannin da suka samu da kuma bada damar yin gwaji ga daukacin mutanen dake cikin fadar.

Garin Daura wadda itace mahaifar shugaban kasa Muhammadu Buhari aka fara samun mai dauke da cutar coronavirus a Jihar Katsina abinda ya sa Gwamna Aminu Bello Masari ya bada umurnin kafa dokar hana zirga zirga a birnin.

Ya zuwa yanzu cutar ta bulla a sassa daban daban na Jihar Katsina wadda yanzu haka ke da mutane 46 da suka kamu da ita, kuma likitan da ya fara kai ta ya mutu.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.