Bakonmu a Yau

Dr Dauda Kwantagora kan yadda Najeriya za ta yi dala miliyan $311 na kudaden Abacha

Sauti 03:38
Tsohon shugaban Najeriya a zamanin mulkin soja marigayi Janar Sani Abacha.
Tsohon shugaban Najeriya a zamanin mulkin soja marigayi Janar Sani Abacha. Issoug Sanogo/AFP/Getty Images

Amurka ta mikawa Najeriya jumillar dala miliyan 311 da dubu 797 da 866 da ake zargin tsohon shugaban kasar marigayi Sani Abacha yashe daga bitalmalin gwamnati.Ministan shari’ar Najeriya Abubakar Malami, ya tabbatar karbar kudaden a yau litinin, cikin sanarwar da ya fitar ta hannun mataimakinsa kan sha’anin kafafen yada labarai Dakta Umar Gwandu.Tuni Yan Najeriya suke ta bayyana farin ciki da samun kudaden a daidai wannan lokaci da tattalin arzikin kasar ke fuskantar barazana, da kuma bada shawarwari kan abinda ya dace ayi da kudaden.Dangane da wannan, Bashir Ibrahim Idris ya tattauna da Dr Dauda Kontagora, masanin tattalin arziki, wanda yayi tsokaci kan mataki na gaba da ya kamata a dauka.