Najeriya-Coronavirus

Gwamnatin Najeriya ta ja kunnen asibitoci kan korar marasa lafiya

Wata likita yayin duba lafiya yaro a wani asibitin kungiyar likitoci na kasa da kasa dake kauyen Bagega, a yankin arewa maso gabashin Najeriya. 14/8/2013.
Wata likita yayin duba lafiya yaro a wani asibitin kungiyar likitoci na kasa da kasa dake kauyen Bagega, a yankin arewa maso gabashin Najeriya. 14/8/2013. REUTERS/Akintunde Akinleye/Files

Gwamnatin Najeriya ta ja kunnen asibitoci da sauran cibiyoyin kula da lafiya a daukacin kasar, da su daina kora ko kin karbar marasa lafiya, musamman ma wadanda ke cikin hali na bukatar agajin gaggawa, saboda tsoron barazanar annobar coronavirus.

Talla

Yayin gargadin a Abuja, Ministan Lafiyar Najeriya Osagie Ehanire yace kin baiwa mara lafiya ya sabawa dokokin Najeriya, musamman a irin wannan lokaci da likitoci gami da sauran jami’an lafiya ke kamuwa da cutar coronavirus da ta addabi duniya, abinda ya haifar da karin matsalar karancin likitocin da dama ake fuskanta a kasar.

Ehanire wanda ya bayyana haka a Abuja, lokacin karin bayani kan halin da ake ciki dangane da yaki da annobar coronavirus a Najeriya, yace a yanzu haka sun mayar da hankali zuwa Kano don taimaka mata wajen yakar annobar, ta fuskoki da dama ciki harda baiwa jami’an ma’aikatar lafiyar jihar karin horo.

Ministan lafiyar Najeriyar, ya kuma sanar da cewa an aike tawagar jami’an lafiya da ta kunshi rukunin jami’an kimanin 20, domin kaiwa ga sassan jihar Kano don yiwa mutane gwajin cutar coronavirus ko COVID-19.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.