Najeriya-Jigawa

Jigawa na bincike kan mutuwar sama da mutane 100 a kwanaki 10

Gwamnan Jihar Jigawa Muhammad Badaru Abubakar.
Gwamnan Jihar Jigawa Muhammad Badaru Abubakar. RFI Hausa/Abubakar Isa Dandago

Rahotanni daga Jihar Jigawa dake Najeriya sun ce sama da mutane 100 sun mutu cikin kwanaki 10 a karamar hukumar Hadeja.

Talla

Samun mace-macen da dama cikin kankanin lokaci, ya sanya Gwamnan jihar Jigawa Alhaji Muhammad Badaru Abubakar, kafa kwamitin gaggawa da ya kunshi mutane 5, domin gudanar da bincike kan lamarin da kuma baiwa gwamnati shawara kan mataki na gaba, kamar yadda kafafen yada labaran Najeriya da dama suka ruwaito ciki harda jaridar Daily Trust da kuma kafar talabijin ta Channels TV.

Yayin karin haske ga manema labarai kan mace-macen bazatar, Sani Kakabori mataimaki na musamman ga shugaban karamar hukumar ta Hadeja, yace mafi akasarin wadanda suka mutu na tsakanin shekaru 50 zuwa 60 ne, kuma akalla mutanen 10 ne suka rika mutuwa kowace rana a tsawon kwanaki 10.

A cikin watan Afrilun da ya gabata, al’ummar Kano suka shaida yawaitar mace-mace kama daga fitattun mutane a jihar zuwa kan saura gama-gari, lamarin da ya jefa firgici a zukatan mutane.

A baya bayan nan ne kuma shugaban tawagar kwararrun likitocin da shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya tura zuwa jihar bayan killace ta da yayi, Dakta Nasiru Sani Gwarzo ya shaidawa sashin Hausa na RFI cewar akwai alaka tsakanin mace-macen da dama da aka samu a Kanon da cutar coronavirus, sai dai ba dukkanninsu ba.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.