Najeriya

Kudaden shigar da Najeriya ke samu daga mai ya ragu da kashi 80

Wasu ma'aikatan hakar mai a filin hakar danyen mai na Bonga dake wajen birnin Legas.
Wasu ma'aikatan hakar mai a filin hakar danyen mai na Bonga dake wajen birnin Legas. REUTERS/Akintunde Akinleye

Gwamnatin Najeriya tace ta samu raguwar kashi 80 cikin 100 na kudin shigar da ta saba samu saboda annobar coronavirus, wadda baki daya ke neman durkusar da tattalin arzikin duniya.

Talla

Babban Daraktan dake kula da ofishin kasafin kudin kasar Ben Akabueze ya bayyana cewa, kasar na asarar kashi 80 na kudaden harajin da take sa ran samu, wanda faduwar farashin mai ya tilasatawa kasar rage hasashen kasafin kudin kasar da aka yi akan dala 57 zuwa dala 20.

Daraktan yace daga cikin kudin man da suke saran samu na naira triliyan kusan 5 da rabi yanzu sun rage shi zuwa triliyan guda da miliyan 120.

Ministan kudin kasar Zainab Ahmed tace yanzu haka Najeriya na fuskantar annoba guda biyu ne da suka hada da COVID-19 da kuma faduwar farashin man fetur.

Najeriya na fitar da gangan mai miliyan biyu kowacce rana amma kuma annobar coronavirus wadda ta shafi harkokin kasuwanci ta sa farashin man ya fadi saboda rufe masana’antu da kuam harkokin yau da kullum.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.