Najeriya-Sokoto

Tsohon Gwamnan Jihar Sokoto ya rasu

Nigeria: Second civilian governor of Sokoto State, Dr Garba Nadama
Nigeria: Second civilian governor of Sokoto State, Dr Garba Nadama Pulse.ng

Allah ya yiwa tsohon Gwamnan Jihar Sokoto dake Najeriya Dakta Garba Nadama rasuwa.

Talla

Tsohon Gwamnan farar hula na 2 a Sokoto, ya rasu a ranar litinin yana da shekaru 82, bayan fama rashin lafiya.

Dr Nadama wanda yayi mataimakin Gwamna ga marigayi Shehu Muhammed Kangiwa tsakanin 1979 zuwa 1982, ya maye gurbinsa sakamakon rasuwar sa a hadarin doki. Marigayi Nadama ya cigaba da jagorantar Sokoto har zuwa shekarar 1983.

Marigayin ya samu shaidar digirin digirgir a tsangayar koyarwa da nazarin tarihi a jami’ar Ahmadu Bello dake Zaria.

A yau talata ake sa ran yiwa tsohon Gwamnan jana’iza.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.