Najeriya

'Yar Adua: Tsohon shugaban Najeriya ya cika shekaru 10 da rasuwa

Tsohon shugaban Najeriya marigayi Umaru Musa Yar'Adua. 14/3/2008.
Tsohon shugaban Najeriya marigayi Umaru Musa Yar'Adua. 14/3/2008. REUTERS/Finbarr O'Reilly

Yau talata tsohon shugaban Najeriya Malam Umaru Musa Yar’Adua ke cika shekaru 10 da rasuwa, inda wasu al’ummar kasar ke tuna irin gudumawar da ya bayar lokacin da ya jagorance su.

Talla

A sakon da ya aike yau, tsohon shugaban kasa Goodluck Jonathan, ya bayyana tsohon mai gidansa a matsayin gwarzon shugaba, adali, mai kishin kasa da kuma irin canjin da ‘yan Najeriya ke bukata.

Shima tsohon ministan yada labarai Ikra Aliyu Bilbis, ya bayyana ‘Yar Adua a matsayin wanda duniya ba za ta manta da shi ba wajen shirin inganta rayuwarsu da kare dimokiradiya, da mutunta ‘yancin dan Adam, da kuma mutunta doka da oda.

An haifi tsohon shugaban Najeriyar a ranar 16 ga watan Agustan shekarar 1951 a Katsina dake Najeriya. Ya samu digirinsa na farko daga jami’ar Ahmadu Bello dake Zaria, daga shekarar 1975 zuwa 1983 kuma ya koyar a Kwalejojin Ilimi da na kimiyya da fasaha, daga bisani kuma ya zama dan kasuwa gami da zama jagora wasu kamfanoni da yayi aiki da su.

Daga shekarar 1991 marigayi Umaru Musa ‘Yar Adua ya mayar da hankalinsa sosai kan siyasa, inda ya tsaya takarar neman kujerar Gwamnan jihar Katsina, amma ya fadi.

Bayan shekaru 7, ‘Yar Adua ya taka muhimmiyar rawa wajen kafa kawancen jam’iyyun Siyasa na K34, da suka yi maja da jamiyyar PDP inda a wannan yanayi ya sake neman kujerar Gwamnan jihar Katsina, ya kuma samu nasarar lashe zaben a 1999, ya kuma yi tazarce a shekarar 2003.

A shekarar 2006, tsohon shugaban Najeriya a lokacin Olusegun Obasanjo, ya zabe shi a matsayin magajinsa, a zaben shugabancin kasar na 2007.

Marigayi ‘Yar Adua ya lashe zaben Najeriyar a shekarar ta 2007, inda a ranar 29 ga watan Mayu na shekarar aka rantsar da shi a matsyin shugaban Najeriya na 13.

A karshen watan Nuwamban shekarar 2009 ‘Yar Adua yayi balaguro zuwa Saudiya domin kula da lafiyarsa, inda ya shafe makwanni ba tare da ji daga gareshi ba.

Ranar 9 ga watan Fabarairun 2010, majalisun dokokin Najeriya suka kada kuri’ar mikawa mataimakin shugaba ‘Yar Aduwa wato Goodluck Jonathan mukamin mukaddashin shugaban kasa, har zuwa lokacin da marigayin zai murmure, lafiyar da tsohon shugaban bai samu ba.

A ranar 5 ga watan Mayu na shekarar 2010 Allah ya yiwa tsohon shugaban Najeriya Umaru ‘Yar Adua rasuwa bayan shafe watanni 3 yana jinya. Ya rasu yana da shekaru 58 a duniya.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.