Najeriya-Coronavirus

Yawan masu cutar coronavirus a Najeriya na gaf da kaiwa dubu 3

Wasu 'yan Najeriya a layin cire kudi daga na'urar ATM a Abuja, bayan sassauta dokar hana zirga-zirgar da a baya aka kafa don dakile yaduwar annobar coronavirus. 4/5/2020.
Wasu 'yan Najeriya a layin cire kudi daga na'urar ATM a Abuja, bayan sassauta dokar hana zirga-zirgar da a baya aka kafa don dakile yaduwar annobar coronavirus. 4/5/2020. REUTERS/Afolabi Sotunde

Hukumomin Najeriya sun sanar da samun adadin wadanda suka kamu da cutar coronavirus mafi yawa na 245 tun bayan da aka samu barkewar cutar a kasar, ranar da aka saki mara ga mazauna biranin Lagos da Abuja da Ogun.

Talla

Alkaluman da hukumar yaki da cututtuka a Najeriya ta bayar sun ce a jiya kawai mutane 245 suka kamu da cutar, yayin da 6 suka mutu, abinda ya kawo adadin wadanda suka kamu da cutar a Najeriya zuwa 2,802, 417 sun warke, 93 sun mutu.

Sabbin kamun sun hada da 76 a Lagos, 37 a Katsina, 32 a Jigawa, 23 a Kano, 19 a Abuja, 18 a Barno, 10 a Edo, 9 a Bauchi, 6-6 a Adamawa da Oyo da Ogun, yayin da aka samu 5-5 a Ekiti da Osun da Benue da Niger, sai kuma Zamfara mai mutum guda.

Har yanzu Lagos ke sahun gaba da yawan mutanen da suka kamu, wadanda suka kai 1,183, sai Kano mai 365, Abuja na da 297, Borno na da 100, Gombe 96, Ogun 85, Katsina 83, Kaduna 81, Bauchi 80, Sokoto 66, Edo 62, Oyo da Jigawa na da 39-39, sai Osun mai 37.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.