Najeriya-Katsina

An garzaya da Sarkin Daura zuwa asibiti

Mai Martaba Sarkin Daura Alhaji Faruk Umar Faruk.
Mai Martaba Sarkin Daura Alhaji Faruk Umar Faruk. Daily Trust

Rahotanni daga jihar Katsina a Najeriya sun ce an kwantar da mai Martaba Sarkin Daura Alhaji Faruk Umar Faruk a babban asibitin gwamnati dake garin Katsina.

Talla

Jaridar ta Daily Nigerian da ta wallafa labarin, ta ce alamun rashin lafiyar dake damun Sarkin a lokacin da aka garzaya da shi asibiti sun yi kama da na cutar COVID-19 ko coronavirus, sai dai wata majiyar tace hawan jini ke damusa.

A ranar litinin da ta gabata, Gwamnan Katsina Aminu Bello Masari ya bada umarnin rufe fadar Sarkin na Daura, matakin da yace ya dauka domin dakile yaduwar annobar ta coronavirus.

Zuwa wannan lokaci dai jumillar masu dauke da cutar coronavirus a Katsina ya kai 75, guda 6 sun warke, yayin da annobar ta kashe mutane 5.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.