Najeriya-Kano

Likitoci 34 sun kamu coronavirus a Kano

Daya daga cikin kayayyakin gwajin cutar Coronavirus.
Daya daga cikin kayayyakin gwajin cutar Coronavirus. REUTERS/Dado Ruvic

Kungiyar likitocin Najeriya reshen Kano, tace manbobinta 34 ne suka kamu da cutar coronavirus a jihar, kuma annobar ta yi sanadin mutuwar daya daga cikinsu.

Talla

Shugaban kungiyar likitocin Dakta Sunusi Bala, ya shaidawa kamfanin dillancin labaran Najeriya cewar, mafi akasarin lkitocin da suka kamu suna aiki ne a asibitin koyarwa na Malam Aminu Kano, sai kuma wadanda ke aiki a wasu asibitoci masu zaman kansu a sassan jihar ta Kano.

Dakta Bala ya kara da cewar, cutar ta coronavirus ta harbi mafi rinjayen likitocin ne a lokacin da suke kan aikin kula da marasa lafiyar da basu nuna alamun sun kamu da cutar ba, sai daga baya gwaji ya tabbatar da hakan.

Shugaban kungiyar likitocin na Kano ya bukaci gwamnati da ta gaggauta basu isassun kyayyakin samun kariya daga cutar coronavirus ko COVID-19 da ake kira da ‘PPE’ a turance, domin karfafa musu gwiwar cigaba da aikin ceton rayukan al’umma.

Kafin aukuwar wannan lamari dai, cikin watan Afrilu Ministan lafiyar Najeriya Osagie Ehanire, ya bayyana cewar ma’aikatan lafiya 113 dake yaki da wannan annobar coronavirus sun kamu da cutar.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.